ALKURANI
Alkurani shi ne littafin da ALLAH subhanahu wa taala ya saukar wa Annabi MUHAMMAD SAW ta hanyar aiko da malaika jibril wanda yake sakko da shi daga lauhul mahfuz zuwa baitul izzah,Kuma karanta shi ibada ne,rubutacce ne a cikin takardu sannan shi ne littafin da ALLAH YA saukar na karshe shi ne babbar muujizar manzon ALLAH.
ALKURANI shi ne babban kundin tsarin mulki na musulmai da shi suke yin sharia kuma shi ne suke karantawa a cikinsalla da kuma wani sashe na ADDUOIN SU.ALKURANI YA kunshi abubuwa da dama kama daga na duniya da na lahira da kissoshin annabawa da kuma salihan bayi littafine wanda ya sauka da harshe larabci.
0 Comments